Garkuwan Cindo ya je Kano buga damben gasar gwamna ta bana

Tsohon Sarkin damben gargajiya Garkuwan Cindo ya sauka a jihar Kano, Nigeria, ranar Asabar domin buga gasar damben Gwamnan jihar Kano ta 2024.

Tun daga ranar Laraba da aka yi bikin karamar Sallah aka fara damben gwamnan jihar Kano, Engineer Abba Kabir Yusuf a filin wasa na Ado Bayero Square a Kano da ake sa ran lashe naira miliyan biyu.

Garkuwan Cindo Guramada ya lashe mota uku a damben Kano, wanda ya sa Guramada ke ji da shi a fannin dambe wajen jarumta da nuna dagiya da kwarewa.

Garkuwan Cindo ya fara daukar mota a damben gwamna a 2018 lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje, bayan da ya buge Ebola a karawar karshe a filin wasa na Kano Pillars da ke Sabon Gari a Kano.

A dai shekarar a damben Sarauta a lokacin Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sunusi, Garkuwan Cindo ya zama zakara bayan da ya yi nasara a wasan karshe da Bahagon Shagon ‘Yan Sanda .

Wannan damben da aka buga a filin wasa na Ado Bayero Square a Kano Bahagon Shagon ‘Yansanda da Garkuwan Cindo yana daya daga wasan da aka buga da ya kayatar a fannin wasan gargajiya a tarihi.

Damben sai dai ya kai turmi uku ana ta yi ba wanda ya fadi, sai da ana daf da tashi a turmin karshe ne Garkuwan Cindo ya buge Bahagon Shagon ‘Yansanda daga Jamus.

Mota ta uku kuwa da Garkuwan Cindo ya dauka ita ce ta Sarauta a 2019, bayan da ya buge Ali Kanin Bello a filin wasa na Ado Bayero Square a Kano, Nigeria.

Cikin manyan ‘yan wasan da ke buga gasar bana har da Bahagon Shagon ‘Yansanda da Ali Kanin Bello da Dogon Dogon Sani da matashi mai tashe Ramadan da fitaccen dan wasan Kudu ‘Yar Mage.

Sakamakon wasannin damben gwamna da aka buga ranar Asabar

  • Shagon Dogon Inda daga Arewa ya doke ya buge Autan Korona daga Kudu
  • Autan Bahagon Balangada daga Jamus ya buge Dogon Korona daga Kudu
  • Bahagon Dage daga Kudu ya yi nasara a kan Mola-Mola daga Arewa wanda ya ji rauni
  • Dogon Dogon Sani daga Arewa ya buge Kurtun Shagon Mada daga Kudu
  • Shagon Gwagwarwa daga Arewa ya buge Shagon Alhazai daga Jamus
  • Shagon Kosilaye daga Kudu ya doke Abba Shagon Roget daga Arewa.

Leave a comment