Fury da Usyk za su dambata a Saudi Arabia

Tyson Fury da Oleksandr Usyk za su dambata ajin babban nauyi a Saudi Arabia ranar 17 ga watan Fabrairun 2024.

Fury dan damben Burtaniya zai saka kambunsa na WBC, yayin da dan Ukraine, Usyk zai saka nasa wato WBA da IBF da kuma WBO.

Duk wanda ya yi nasara a ranar zai kwashe dukkan kambunan hudu a fafatawar da za a yi a Riyadh.

Kuma duk wanda ya lashe kambunan zai zama na farko a tarihi tun bayan bajintar da Lennon Lewis ya yi a 1999 zuwa 2000.

Tun farko an tsara yin damben tsakanin Fury, mai shekara 35 da Usyk, mai shekara 36 ranar 23 ga watan Disamba.

An daga wasan zuwa Fabrairun badi, bayan Fury ya yi nasara a kan Francis Ngannou a watan jiya.

Fury din ya ji ciwo a goshinsa, sannan daya idonsa ya kumbura, hakan ya sa aka dage karawar.

Dan damben Burtaniya na fatan yin nasara karo 34 da canjaras daya, tun bayan da ya zama kwararren dan damben boksin a 2008.

Saudi Arabia ta karbi bakuncin manyan wasan damben boksin a baya, ciki har da wanda Usyk ya doke Anthony Joshua a 2022.

Leave a comment