Frankfurt ta dauki aron Van de Beek daga Manchester United

Eintracht Frankfurt ta dauki aron dan kwallon tawagar Netherlands, Donny van de Beek daga Manchester United, kamar yadda kungiyar da ke buga Bundesliga ta sanar yau Litinin.

Ta kulla yarjejeni da United mai buga Premier League cewar dan kwallon zai taka leda a kungiyar zuwa karshen kakar bana.

Van de Beek ya buga wa Man United wasa 62 a dukkan karawa da cin kwallo biyu, tun bayan da ya koiyarma Old Trafford daga Aajax a Satumbar 2020.

Leave a comment