France ta gayyaci Kante zuwa Euro 2024

Tawagar Frane ta gayyaci N’Golo Kante daga cikin yan wasan da koci Didier Deschamps ya bayyana don buga Euro 2024.

Kante, mai shekara 33, ya taka rawar gani da ta kai France ta lashe kofin duniya a Rasha a 2018, sai dai rabonda ya buga wa kasar tamaula tun Yunin 2022, sannan ya koma Al-Ittihad ta Saudi Arabia da taka leda.

Kante ya yi fama da jinya a daf da zai bar Chelsea, sai dai kociyan France, Deschamps ya ce dan kwallon yana da tarin kwarewar da zai taimaka musu a Germany.

Haka kuma matasan ‘yan wasan dake taka leda a Paris St Germain, Warren Zaire-Emery, mai shekara 18 da Bradley Barcola, mai shekara 21 suna cikin wadanda za suje Germany a bana.

Haka kuma Deschamps ya bayyana Kylian Mbappe da Antoine Griezmann da Olivier Giroud da mai tsaron bayan Arsenal, William Saliba cikin tawagar.

France tana cikin wadanda ake cewa za ta taka rawar gani a Germany, wadda ke fatan daukar Euro na uku, bayan da ta lashe kofin a 1984 da kuma 2000.

France za ta fara da Austria a Stuttgart ranar 17 ga watan Yuni.

‘Yan kwallon tawagar France

Masu tsaron raga: Alphonse Areola (West Ham), Mike Maignan (AC Milan), Brice Samba (Lens)

Masu tsaron baya: Jonathan Clauss (Marseille), Ibrahima Konate (Liverpool), William Saliba (Arsenal), Jules Kounde (Barcelona), Theo Hernandez (AC Milan), Ferland Mendy (Real Madrid), Benjamin Pavard (Bayern Munich), Dayot Upamecano (Bayern Munich)

Masu buga tsakiya: N’Golo Kante (Al-Ittihad), Eduardo Camavinga (Real Madrid), Adrien Rabiot (Juventus), Antoine Griezmann (Atletico Madrid), Aurelien Tchouameni (Real Madrid), Warren Zaire-Emery (Paris St-Germain), Youssouf Fofana (Monaco)

Masu cin kwallaye: Kylian Mbappe (Paris St-Germain), Bradley Barcola (Paris St-Germain), Ousmane Dembele (Paris St-Germain), Kingsley Coman (Bayern Munich), Marcus Thuram (Inter Milan), Randal Kolo Muani (Paris St-Germain), Olivier Giroud (AC Milan)

Leave a comment