Flamengo ta sallami kocinta Luis duk da doke Madureira 8-0

Ƙungiyar Flamengo ta Brazil ta kori mai horar da ita, Filipe Luis tsohon ɗan wasan Chelsea da Atletico Madrid kwana ɗaya tsakani bayan cin gasar kofi a zagayen daf da karshe da jimilla ƙwallaye 11-0.

A ranar Litinin, Flamengo ta doke Madureira 8-0, sai dai ƴan mintoci kaɗan bayan wasa aka sallami, Luis.

Wannan ba ƙaramin abin mamaki bane domin Luis ya jagoranci Flamengo zuwa lashe gasar Brazilian league da Copa Libertadores a baya

To sai dai Flamengo ta fara kakar wasa ta bana a matakin mafi muni cikin shekara goma. Ta sha ɗaukar a gasar Brazilian ta Super Cup da South American Super Cup sannan suka fara kakar bana a lik da nasara ɗaya da canjaras ɗaya aka doke ta wasa ɗaya.

Ƙungiyar na wannan rashin kokarin duk da sayen Lucas Paqueta da wasu ƴan ƙwallon da ta kashe fam miliyan 5.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top