Finalissima: An soke wasan Spain da Argentina a Qatar

An soke wasan da ya kamata a fafata tsakanin tawagar Sifaniya da ta Argentina a Qatar, saboda yaƙi da ake yi a Gabas ta tsakiya.

Wasan Finalissima da ake yi duk shekara huɗu tsakanin mai rike da kofin nahiyar Turai da Sifaniya ce gwarzuwa da Argentina mai Copa America, mai rike da kofin Kudancin Amurka.

Tun farko an tsara yin gumurzun ranar 26 ga watan Maris, sai dai kuma hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa ta ce Argentina ta yi watsi da tayin da aka yi mata na a buga wasan falle biyu a Santiago Bernabeu da kuma a birnin Buenos Aires.

Wani rahoto da hukumar ƙwallon kafar Kudancin Amurka ta fitar, Conmebol ta ce ta bayar da shawarar a buga wasan ranar 31 ga watan Maris, amma Uefa ba ta amince da hakan ba.

Daga nan ne hukumar ƙwallon kafa ta Turai ta ce ba zai yiwuba a buga fafatawar kwana huɗu tsakani daga ranar da aka tsara tun farko ba, saboda haka an soke Finalissama na wannan karo.

Ana buga Finalissma duk bayan shekara huɗu, kuma Argentina ce ta lashe wanda aka yi a 2022 a Wembley.

Sakamakon yaƙin da ake yi a Gabas ta tsakiya ana ta soke manyan wasannin da ya kamata a buga daga ciki har da tseren motocin Formula 1 da aka tsara yi a Bahrain da Saudiyya a cikin watan Afirilu.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top