Fifa World Club Cup: Man City da Urawa Red Diamonds

Za a buga wasan daf da karshe a Fifa World Club Cup tsakanin Manchester City da Urawa Red Diamonds ranar Talata.

Manchester City ita ce mai rike da Champions League, ita kuwa Urawa ta lashe Asia Cup na bara.

Haka kuma kungiyar Japan ta yi nasarar doke Club Leon ta Mexico 1-0 ranar Juma’a a Saudi Arabia.

Duk wadda ta yi nasara za ta kara da Fluminense a wasan karshe, wadda ta ci Al Ahly 2-0 ranar Litinin a karawar daf da karshe.

An tsara cewar daga 2025 Fifa World Club Cup zai koma kungiyoyi 32 da za su rika buga gasar.

City ce ke rike da Premier League da Champions League da FA Cup da Uefa Super Cup ta kuma lashe EFL Cup da Community Shield karkashin Pep Guardiola.

Man City ta ziyarci Saudi Arabia tare da Kevin de Bryne da kuma Erling Haaland, domin buga wasan daf da karshen.

Rabonda De Bryne ya taka leda tun wasan farko na bude gasar bana, bayan rauni da ya ji, amma ya yi atisaye ranar Litinin.

Shi kuwa Haaland wasa uku ne bai yi ba, sakamakon jinya da yake yi.

Kofi 10 a Fifa World Club Cup, kungiyoyin nahiyar Turai ne ke lashewa har da wanda Liverpool da Real Madrid da Chelsea da kuma biyun da Pep Guradiola ya dauka a Barcelona.

Leave a comment