Fernandez ya gama buga wa Chelsea wasannin bana

Likitoci sun kammala yi wa dan wasan Chelsea, Enzo Fernandez, ba zai buga wa kungiyar saura wasa shidan dake gabanta ba.

Dan kasar Argentina ya kama da ciwon kaba cikin Disambar 2023, wanda ya fara wasan da Arsenal ta dura 5-0 a ragar Chelsea ranar Talata a Premier League daga baya aka sauya shi a zagaye na biyu.

Mai shekara 23 zai yi jinya karkashin kulawar likitocin Chelsea a Cobham.

Rashin Fernandez a Chelsea koma baya ne ga kungiyar wadda take ta tara a teburin Premier League, wadda ranar Asabar za ta kara da Aston Villa, wadda take ta hudun teburin babbar gasar tamaula ta England.

To sai dai tawagar Argentina na fatan Fernandez zai warke da wuri, domin ya samu buga mata Copa America da za ta yi a Amurka cikin watan Yuni da Yuli.

Leave a comment