FA Cup: Manchester United ta kai wasan karshe

Manchester United ta kai wasan karshe a FA Cup na kakar nan, bayan da ta fitar da Coventry City a bugun fenariti a Wembley ranar Lahadi.

Tun farko United ce ta fara zura uku a raga ta hannun Scott McTominay da Harry Maguire da kuma Bruno Fernandes.

Daga baya kungiyar dake buga championship ta farke ukun ta hannun Ellis Simms da Callum O’Hare, sannan Haji Wright ya zura a raga a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Daga nan suka je karin lokaci, sannan ta kai su ga bugun fenariti, inda kungiyar Old Trafford ta ci 4-2.

United mai FA Cup 12 za ta buga wasan karshe da Manchester City mai rike da na bara mai bakwai da za su fafata a Wembley.

Wannan shi ne karo na biyu da kungiyoyi za su buga wasan karshe a FA Cup sau biyu a jere, bayan Blackburn Rovers da ta doke Queen’s Park a Kennington Oval a 1884 da kuma kakar 1885.

City ce ta doke United 2-1 a bara a Wembley, inda IIkay Gundogon ya zura biyu a raga, sannan Bruno Fernandes ya zare daya a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Leave a comment