FA Cup: Manchester City da Chelsea a Wembley

Manchester City da Chelsea za su kara a FA Cup zagayen daf da karshe ranar Asabar a Wembley.

Wannan shi ne karo na uku da za su fafata a bana, bayan da suka fara tashi 4-4 a Premier League cikin Nuwamba a Stamford Bridge, sannan suka yi 1-1 a Etihad cikin Fabrairu a babbar gasar tamaula ta England.

2023/2024

Premier League Asabar 17 ga watan Fabrairu     

  • Man City         1 – 1     Chelsea          

Premier League Lahadi 12 ga watan Nuwamba              

  • Chelsea           4 – 4     Man City

Sai dai wannan shi ne karo na tara da za su kece raini a FA Cup, yayin da Manchester City mai rike da na bara ta ci wasa biyar, Chelsea ta yi nasara uku ba canjaras a tsakaninsu.

Tun farko Manchester City ta sa ran lashe kofi uku a bana kamar yadda ta yi a bara ta dauki Premier League da FA Cup da kuma Champions League, amma Real Madrid ta fitar da ita a gasar bana a Etihad a bugun fenariti.

City ce ta daya a kan teburin Premier League da maki 73, sai Arsenal ta biyu mai maki 71, iri daya da na Liverpool ta uku.

Chelsea tana mataki na tara a teburin Premier League da maki 47, kuma FA Cup ne kadai take fatan dauka a bana, bayan da Liverpool ta yi nasara a kanta a Carabao Cup a wasan karshe a kakar nan.

Kenan City tana sa ran lashe FA Cup da Premier League kenan a kakar nan, yayin da Chelsea wadda karo na biyu a jere da ba za ta je gasar zakarun Turai ba ke fatan daukar FA Cup.

Kungiyar Stamford Bridge tana da FA Cup takwas jimilla, yayin da wadda take Etihad tana da bakwai.

Daya wasan daf da karshe za a buga ne tsakanin Coventry City da Manchester United a Wembley ranar Lahadi.

Leave a comment