European Super League: Barcelona da Real Madrid za su samu ladan £869

Barcelona da Real Madrid za su samu ladan £869 idan har za a gudanar da European Super League.

Tun farko wasu manyan kungiyoyi 12 ne suka kulla yarjejeniyar kirkira gasa a Turai a cikin Afirilun 2021, daga baya 10 daga ciki suka janye aka bar kungiyoyin Spain biyu a fafutuka.

Kamfanonin da suka so zuba jari suka janye daga tsarin, bayan da ‘yan kallo suka caccaki shirin, sannan gwamnati taki amincewa da kirkirar European Super League.

Daga nan ne Fifa da Uefa ta yi barazanar hukunta kungiyoyi da ‘yan wasan da za su buga sabuwar gasar.

To sai dai Barcelona da Real Madrid sun ci gaba da gwagwar maya, har da zuwa kotu, wadda ta yanke hukuncin a makon jiya da ya kara musu kwarin gwiwa.

Kamfanin A22 Sports daya daga cikin da ya rage da zai samar da kudi da kungiyoyin Spain biyu suka kai Fifa da Uefa kara kan batun hukunta kungiya da ‘yan wasa, inda kotu ta ce hakan bai dace ba.

Masu son kafa sabuwar gasar na cewar ita ce babbar hanyar ci gaban tamaula ta hanyar kasuwanci da kuma ‘yan kallo, duk da cewar magoya baya tamaula a duniya na tur da tsarin.

Bayan da kotun ta yanke hukuncin kamfanin A22 Sports ya sanar da fasalin Super League da cewar za ta kunshi kungiyar kwallon kafa ta maza 64 da ta mata 32 tsakanin manyan gasa uku ta Turai da kamfanoni 12 za su samar da kudin gudanarwa.

Har yanzu ana wadai da tsarin har da wasu manyan kungiyoyin Turai da gasar Premier League musamman manya shida da kuma AC Milan da Inter Milan da Atletico Madrid.

Barcelona da Real Madrid sun fitar da sanarwa cewar suna nan kan bakansu, za kuma su ci gaba da gwagwarmaya, yayin da A22 Sports ya ce zai ci gaba da kokarin shawo kan Premier League da wasu kungiyoyin.

Kamar yadda A22 Sports ya sanar, idan har aka samu nasarar kafa sabuwar gasar Super League – Barcelona da Real Madrid za su samu £868.9m, saboda jajircewarsu.

Leave a comment