Europa League: Akwai jan aiki a gaban Liverpool a gidan Atalanta

Liverpool ta yi rashn nasara a hannun Atalanta da ci 3-0 a wasan farko a quarter finals a Europa League a Anfield.

Minti na 38 da fara wasan Atalanta ta fara zura kwallo ta hannun, Gianluca Scamacca haka suka je hutu kungiyar Italy na cin kwallo 1-0.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Gianluca Scamacca ya kara na biyu, sannan Mario Pasalic ya zura na uku a raga, saura minti bakwai a tashi daga karawar.

Ranar Alhamis 18 ga watan Afirilu Atalanta za ta karbi bakuncin Liverpool a wasa na biyu a Europa League a zagayen daf da na kusa da na kashe.

Duk wadda ta yi nasara za ta fuskanci Benfica ko kuma Marseille a zagayen daf da karshe, kungiyar Portugal ta ci ta France 2-1 a wasan farko ranar Alhamis.

Atalanta tana ta shida a teburin Serie A da tazarar maki 32 tsakaninta da AC Milan, wadda take jan ragama, ita kuwa Liverpool tana ta biyu a teburin Premier League da maki 71 iri daya da na Arsenal ta daya.

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya sauya ‘yan wasa shida daga wadanda ya fuskanci Manchester United har suka tashi 2-2 a Premier League a karshen makon da ya wuce.

Leave a comment