EURO 2024: Watakil a hada England da Scotland da Wales rukuni daya

Watakila a hada England da Scotland da Wales a rukuni daya, idan an zo raba jadawalin Euro 2024 ranar Asabar.

Za a gudanar da bikin a birnin Hamburg a Jumus, wadda za ta karbi bakuncin wasannin da za a kara a badi.

England, wadda ta yi ta biyu a Euro 2020 ana saka ta cikin wadanda ake hangen za ta iya daukar kofin nahiyar Turai a 2024.

Ana kuma sa ran matasanta za su taka rawar gani, musamman Jude Bellingham mai taka leda a Real Madrid.

England, wadda ta samu gurbin shiga gasar kai tsaye a rukunin da yake da Italy, ya sa an saka tawagar cikin fitattun farko a gasar.

Wasu kuma na cewar wannan ce babbar gasa da Gareth Southgate zai ja ragama ta karshe, bayan da yarjejeniyarsa zai kare a karshen Disambar 2024.

Bayan da England take tukunyar farko, Scotnald tana ta uku, Wales, wadda za ta yi karawar cike gurbi tana tukunya ta hudu idan ta kai labara.

Yadda aka watsa kasashen a tukwane da dan-da ban ya sa ana ganin za su iya fuskantar juna a rukuni daya a 2024.

England ta fuskanci Scotland a karawar cikin rukuni a Euro 2020, haka kuma England an hada ta rukuni daya da Wales a gasar kofin duniya a Qatar a 2022.

Haka kuma a hada England da Wales a cikin rukuni na Euro 2016.

Leave a comment