Euro 2024: Liechtenstein za ta kara da Portugal

Liechtenstein za ta karbi bakuncin Portugal a filin wasa na Rheinpark a karawar neman shiga Euro 2024 da za su fafata ranar Alhamis.

Mai masaukin baki ta yi rashin nasara a wasa takwas da ta yi a cikin rukuni, ita kuwa Portugal tana jan ragama a matakin farko.

Liechtenstein ta yi rashin nasara da ci 4-0 a hannun Iceland a wasan baya a cikin rukuni, ita kuwa Portugal zuwa ta yi ta doke Bosnia and Herzegovina 5-0 a watan jiya.

Cikin wadanda suka ci mata kwallaye har da Cristiano Ronaldo mai biyu sai kuma Bruno Fernandes da João Félix da kuma João Cancelo.

Tuni dai Portugal ta samu gurbin buga gasar Euro 2024 da za a buga a Jamus tsakanin Yuni zuwa Yulin 2024.

Me kuke son sani kan wasan Liechtenstein da Portugal?

Tawagogin biyu sun kara sau takwas a tsakaninsu, biyar daga ciki a wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Turai suka yi.

Portugal ta yi nasara sau bakwai a kan Liechtenstein a haduwa takwas da suka yi a dukkan fafatawa.

Cikin wasa takwas da suka yi a tsakaninsu, Portugal ta ci Liechtenstein kwallo 39-3.

A cikin watan Maris a wasan farko na cikin rukuni, Portugal ta yi nasara cin 4-0.

Sauran wasannin neman shiga Euro 2024 ranar Alhamis:

Georgia da Scotland   

Estonia da Austria       

Azerbaijan da Sweden

Cyprus da Spain

Bulgaria da Hungary

Montenegro da Lithuania             

Luxembourg da Bosnia And Herzegovina       

Slovakia da Iceland

Leave a comment