Eriksen ya koma atisaye a Manchester United

Christian Eriksen ya koma yin atisaye a Manchester United, bayan jinya da ya sha.

Mai shekara 31 ya yi jinyar mako biyar, bayan raunin da ya ji a gwiwa a karawar da United ta ci Luton 1-0 a Premier League.

An ga Eriksen na motsa jiki a Carrington, wurin da kungiyar ke atisaye kwana daya tsakani da Manchester United ta tashi 0-0 da Liverpool a Anfield.

Samun saukin dan kasar Denmark zai kara karfin kungiyar Man United mai fama da ‘yan wasa da yawa da ke jinya.

Wasu da ke jinya a kungiyar Old Trafford sun hada da Casemiro da Lisandro Martinez da kuma Tyrell Malacia.

Harry Maguire da Mason Mount da Victor Lindelof da kuma Amad Diallo suma na jinya.

Shi kuwa Anthony Martial bai yiwa Man United wasan da ta ziyarci Anfield ba ranar Lahadi.

Leave a comment