Enrique ya gaji da amsa tambaya kan Mbappe

Kociyan Paris Saint-Germain, Luis Enrique ya ce ya gaji da amsa tambaya kan dalilin da yake fara wasa ba tare da Kylian Mbappe ko kuma canja shi a wasanni.

Tun bayan da kyaftin din tawagar France ya sanar da cewar zai bar PSG a karshen kakar nan, Enrique ke canja Mbappe, wani lokacin ma ba za a fara wasa da shi ba.

A baya dai PSG kan yi amfani da Mbappe a dukkan kakar tamaula tun daga 30 ga Satumba zuwa 2 ga watan Afirilu, wanda ya buga minti 90 a karawa 14.

Amma a yanzu wasa daya kacal ya yi minti 90 daga bakwai baya da ya yiwa PSG.

Tun a baya kociyan PSG ya sanar cewar ya dauki mataki ne, domin kungiyar ta saba wasa ba tare da Mbappe ba, wanda ya yanke shawarar Real Madrid zai koma da taka leda.

Leave a comment