Ederson ba zai buga wasan karshe a Premier da FA Cup ba

Mai tsaron ragar Manchester City ba zai buga wasan karshe a Premier League da FA Cup, bayan raunin da ya ji a idonsa.

Dan kwallon tawagar Brazil, mai shekara 30 bai ji dadi ba da aka sauya shi a minti na 69 ranar Talata a gasar Premier da City ta je ta doke Tottenham 2-0, bayan da ya yi karo da Cristian Romero.

City, wadda take ta daya a kan teburin Premier League za ta karbi bakuncin West Ham ranar Lahadi 19 ga watan Mayu a wasan karshe na rufe gasar.

Da zarar City ta lashe wasan za ta lashe Premier League na hudu a jere, za ta kafa tarihin da ba wadda ta taba yin wannan bajintar a babbar gasar tamaula ta Ingila.

A kuma ranar Arsenal, wadda take ta biyun teburi da tazarar maki biyu za ta karbi bakuncin Everton, bayan da Gunners ke fatan daukar Premier League a karon farko tun bayan shekara 20.

Daga nan City za ta fafata da Manchester United a wasan karshe a FA Cup ranar 25 ga watan Mayu a Wembley.

Mai tsaron raga, Stefan Ortega, wanda ya yi kokari sosai a wasan Tottenham shi ne zai maye gurbin Ederson, wanda zai karasa wasa biyun dake gaban City a bana, wadda ke fatan lashe kofi biyu a bana.

Dan kasar Germany shi ne yake kamawa City gola a FA Cup da kuma Carabao Cup a kaka biyu da ta wuce, wanda ya shirya tsare ragar kungiyar a wasan karshe a FA Cup koda Ederson ya warke.

Leave a comment