Duk masu zagina ba su san kwallo ba – Jackson

Dan wasan Chelsea, Nicolas Jackson ya ce dukkan masu zaginsa ba su san kwallon kafa ba.

Chelsea ta dauko dan wasan tawagar Senegal daga Villareal kan £32 duk da cewar ba wata gagarumar rawar da ya taka a Spain.

Mai shekara 22 ya bayar da gudunmuwar cin kwallo takwas a kakar farko a Chelsea da bayar da daya aka zura a raga a wasa 15 da canji hudu a dukkan fafatawa.

Koda yake ya ci kwallo a wasa da Sheffield a karshen mako na biyu kenan a wasa shida tun bayan da ya zura uku rigis a ragar Tottenham a karshen watan Nuwamba.

To sai dai Jackson na nuna fushinsa a fili idan yana taka leda, wanda ya karbi katin gargadi bakwai.

Haka kuma an yi mamaki da FA ba ta hukunta dan wasan ba, wanda ya shake wuyan Nathan Patterson a karawar da Everton ta doke Chelsea 2-0 a wasan mako na 16 a Premier.

Maimakon dan wasan ya yadda da sukar da ake masa, Jackson ya ce bai damu da duk abinda za a ce a kansa ba.

‘’Ba zan saurari duk wata magana ba, indai ba daga bangaren Chelsea take ba – ta zama zancen banza.’’

Ya kara da cewar ‘’Ya kamata na ci kwallo da yawa ina barar da damarmaki, amma daga La Liga na koma Premier League akwai banbanci, ina iya kokari na.’’

Wasu rahotanni na cewar Chelsea za ta shiga kasuwa a cikin watan Janairu, domin sayo mai cin kwallo da zai yi gogayya da Jackson da kuma Armando Broja.

Leave a comment