Dortmund ta doke PSG ta kai wasan karshe a Champions League

Borussia Dortmund ta samu gurbin buga wasan karshe a Champions League, bayan da ta doke Paris St Germain da cin 1-0 a Parc des Prince.

Kungiyar Jamus ta kai wannan matakin, bayan da ci 1-0 a ranar Laraba ta makon jiya, kenan ta kai zagayen gaba da cin 2-0 gida da waje.

Tun farko sun je hutu ba ci, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Dortmund ta zura kwallo a raga ta hannun Mats Hummels, wannan shi ne karon farko da za ta buga wasan karshe tun bayan 2013.

Dortmund ta taba lashe Champions League a karon farko a 1996/97.

Wannan shi ne karo na hudu da suka fafata a Champions League a bana, bayan da suka hadu a rukuni na shida, inda PSG ta ci 2-0 cikin Satumba, sai suka tashi 1-1 a Jamus a cikin Disamba.

Watakila Dortmund ta fuskanci takwararta daga Jamus, Bayern Munich mai Champions League shida ko kuma Real Madrid mai 14 jimilla.

Ranar Laraba za a fafata a wasa na biyu a gasar zakarun Turai tsakanin Real Madrid da Bayern Munich a zangon daf da karshe a Santiago Bernabeu.

Ranar Talata ta makon jiya suka tashi 2-2 a Allianz Arena.

Za a buga wasan karshe a Champions League na bana ranar 1 ga watan Yuni a Wembley.

Leave a comment