Dortmund ta ci PSG a Champions League a Germany

Borussia Dortmund ta yi nasara a kan Paris St Germain 1-0 a wasan farko na daf da karshe a Champions League da suka kara a Germany.

Dortmund ta ci kwallon ta hannun Niclas Fullkrud a minti na 36 da wasan da suka yi ranar Laraba.

Wannan shi ne karo na bakwai da suka kara a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, inda Dortmund ta yi nasara ta biyu iri daya da ta PSG da canjaras uku a tsakaninsu.

PSG, wadda ta lashe Ligue 1 na bana za ta karbi bakuncin karawa ta biyu ranar Talata 7 ga watan Mayu a France.

Dortmund ta taba lashe Champions League a 1996/17, ita kuwa PSG ba ta taba daukar kofin ba.

Kylian Mbappe na fatan lashe Champions League a bana a PSG. a karon farko a tarihin kungiyar, wanda zai koma Real Madrid da taka leda a karshen kakar nan.

Leave a comment