Doma United ta ci gaba da zama ta daya a Firimiyar Nigeria

Doma United ta ci Kano Pillars 1-0 a wasan mako na 13 a gasar Firimiyar Nigeria ranar Asabar.

Doma ta ci kwallon ta hannun Ekpenyong, kenan kungiyar ta yi wasa tara ba tare da an doke ta ba.

Haka kuma karo na tara a jere da kwallo bai shiga ragar kungiyar ban a 11 jimilla.

Da wannan sakamakon Doma United tana ta daya da maki 25, sai Remo ta biyu mai maki 23 iri daya da na Lobi Stars ta uku.

Enyimba maki 19 ne da ita iri daya da na Kano Pillras ta biyar din teburi, bayan karawa 13.

Sai a ranar Lahadi 10 ga watan Disamba za a buga karawa tara a sauran filaye a fadin kasar.

Leave a comment