Djokovic zai fuskanci Tsitsipas a atp fINALS A BIRNIN tURIN

Wanda yake na daya a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon tennis a duniya, Novak Djokovic anhada shi rukuni da Stefanos Tsitsipas da Jannik Sinner da Holger Rune a ATP Finals a Turin.

Daya rukunin ya kunshi zakaran Wimbledon, Carlos Alcaraz da Daniiol Medvedev da Andrey Rublev da wanda ya lashe Olympic, Alexander Zverev.

Ana buga ATP Finals tsakanin ‘yan wasan tennis da ke takwas din farko a kakar wasa, wadanda ake raba su rukuni biyu dauke da ‘yan wasa hurhudu kowanne.

Biyan da suka yi fice a kowanne rukuni su kai zagayen daf da karshe.

Za a fara wasannin ranar Lahadi, sannan a buga karawar karshe ranar 19 ga watan Nuwamba.

Bayan da Djokovic ya lashe Paris Masters kofi na 40 jimilla, na fatan dauka ATP Finals na bakwai, hakan zai yi kan-kan-kan da Roger Federer.

Coming off a 40th Masters title on the weekend in Paris, Djokovic is aiming for a record seventh trophy at the ATP Finals which would break a tie with Roger Federer.

Zverev ya lashe kofin karo biyu, yayin da Medvedev da Tsitsipas kowanne yake da guda-guda.

Leave a comment