Djokovic ya rabu da koci Ivanisevic

Wanda yake na daya a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon tennis a duniya, Novak Djokovic ya sanar cewar ya raba gari da koci, Goran Ivanisevic.

Djokovic da kociyansa sun yi aiki tare da dan kasar Serbia ya samu nasarori da yawa a fannin kwallon tennis a duniya.

Ivanisevic ya zama kocin Djokovic cikin Maris din 2022, bayan da ya gama aiki da wanda dan kasar Serbia ke kwaikwayo, Marian Vajda.

Wanda yake na daya a kwallon tennis a duniya, ya sanar da raba gari da kocin nasa a kafar sada zumunta ta Instagram.

Djokovic ya taka rawar gani a kakar da ya fi kwazo a 2023, wanda ya lashe Grand Slam uku, wanda ya rasa kofin Wimledon a hannun Carlos Alcaraz.

Ya yi rashin nasara a karon farko a Australian Open a 2018 a hannun Jannik Sinner, sannan ya sha kashi a hannun Luca Nardi a Indian Wells a cikin watan Maris daga baya ya sanar cewar ba zai shiga Miami Open ba.

Leave a comment