Davis Cup 2023: Sinner ya doke Djokovic

Jannik Sinner ya doke Novak Djokovic a wasan kusa da na karshe a Davis Cup, da aka yi tsakanin Italiya da Serbia a yau asabar.

Serbia ce akan gaba a zagayen farko na wasan da ci 6-7 (7-9) 6-2 6-1.

Sai dai Sinner ya nuna ajin sa inda ya doke na daya a duniya wato Djokovic da ci 6-2 2-6 7-5, ya mayar da wasan kunnen doki.

Daga nan Sinner da Lorenzo Sonego suka doke Djokovic da Kecmanovic da ci 6-3 6-4 a wasan mutum biyu.

Italiya ta samu gurbi a wasan karshe, da za’ayi ranar Lahadi 26 Nuwamba, 2023 da Kasar Australia.

Leave a comment