Daraktan wasannin Man United zai matsa ya bayar da wuri

Manchester United ta sanar cewar daraktan wasanninta, John Murtough zai ajiye aikin, inda take daf da kawo madadinsa.

Wannan yana daga cikin tsare-tsare da ake yi a Old Trafford, domin kara daga darajar kungiyar tun bayan da Sir Jim Ratcliffe ya mallaki wani kaso na hannun jarin kungiyar.

United na shirin kawo daraktan wasannin Newcastle United, Dan Ashworth da na Southampton, Jason Wilcox, hakan ya sa dole Murtough ya hakura da aikin, bayan shekara 11 da ya yi a kungiyar.

Murtough ya je United daga Premier League cikin 2013 daga nan ya koma mai kula da ci gaban tamaula a kungiyar, wanda ya kai matakin daraktan wasannin a Maris din 2021.

United, wadda ke fatan bai wa Ashwort aikin har yanzu ba ta kai ga kulla kwantiragi da Newcastle ba, wadda a watan Fabrairu ta amince daraktan nata ya tattauna da kungiyar Old Trafford.

Haka kuma har yanzu United ba ta kai ga kulla yarjejeniya da Wilcox daga Southampton ba.

Leave a comment