Dan Yalo ya kasha Autan na Aisha a damben naira 100,000

Ranar Lahadi Autan na Aisha wanda ya yi sama da wata bakwai bai fadi ba a Maraba dan Yalon Tula ya buge shi.

Dambe ne na naira 100,000 tsakanin Dan Yalo daga Arewa da Autan na Aisha Guramada a Marabar Nyanya jihar Nasarawa.

A turmi na biyu dan wasan Arewa ya yi nasara a kan dan damben Guramada, wanda ya dade a tsaya ba tare da an buge shi ba.

Mako mai zuwa za a yiwa Autan na Aisha Ajo a Marabar Nyanya, daga nan zai je gida ya huta, sannan ya kara wani shirin.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Bahagon Ali Kawoji ya buge Shagon Aliyu.

Autan Kudawa da Ghali Shagon Mai takwasara suka tashi canjaras, haka ma wasan Shagon Autan Dan Bunza da Alaye ba kisa.

Shi kuwa Dogon Mamman buge Shagon Basiru ya yi, Rabe Bahagon Ebola ya yi nasara a kan Dan Aliyun Arewa.

Ilele Garkuwan mai Caji ya doke Garkuwan Yahayan Tarasa da canjaras tsakanin Shagon Duna da Shagon Lawwalin Gusau.

Leave a comment