damben naira 100,000 tsakanin Bahagon Kawoji da Ilele

Kungiyar dambe ta kasa reshen jihar Nasarawa a Nigeria ta tsara damben gasa guda hudu da za a yi ranar Lahadi da safe

Wasannin da za a gudanar a ‘yan tifa a marabar ‘Nyanya, kowanne za a dambata ne kan naira 100,000.

Wasannin sun hada da na Autan Na Aisha da Bahagonr Autan Mamman daga Jamus.

Shi dai Autan na Aisha Guramada ya fi wata biyar har yanzu bai fadi ba, wanda an kawo masa ‘yan dambe da yawa ko dai a yi canjaras ko ya yi kisa.

Haka kuma akwai wasa tsakanin Rabe Bahagon Ebola daga Kudu da na Dan Yalon Tula daga Arewa.

Bayan nan za a sa zare tsakanin Garkuwan Kurma Guramada da Garkuwan Duna daga Kudu.

Shi dai Garkuwan Dunan ba ta jemu ba tsohon dan wasan Guramada ne, yanzu ya koma Kudu.

Wasa mai zafi kuwa da za a buga shi ne tsakanin Ilele Shagon Garkuwan mai Caji da Bahagon Ali Kawoji.

Tun bayan da Bahagon Ali Kawoji ya sauka a Marabar ‘Naynya a buge Rabe Shagon Ebola da Dan Aliyu na Arewa a damben Lahadi-Lahadi.

Wasannin da za a buga ranar Lahadi:

  • Autan na Aisha da Bahagon Autan Mamman
  • Rabe Bahagon Ebola da Dan Yalon Tula
  • Ilele Garkuwan Mai Caji da Bahagon Ali Kawoji
  • Garkuwan Kurna da Garkuwan Duna

Leave a comment