Damben Kano: Autan Mamman da Yahayan Tarasa ba kisa

An buga wasa da yawa ranar Alhamis a damben Kano da aka yi a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Nigeria.

Wasa ɗaya aka buga a damben gwamnan jihar Kano, shi ne tsakanin Autan Bahagon Inda da Garkuwan Hadejia.

An kuma yi damben Kasuwa inda Oris ya buge Shagon Shagon Audun Tunga da na Guramaɗa ɗan kasa da gudumar Autan Mamman ba kisa.

An kuma yi canjaras tsakanin Bahagon Ramadan da Shagon Garkuwan Cindo da na Shagon Junior Ramadan da Dogon Shagon Guramaɗa.

Daga karshe aka rufe da damben Autan Mamman da Yahayan Tarasa, wasa ne na turmi biyu tsakanin ɗan wasan Jamus da na Guramaɗa.

Ƴan kallo sun yi fatan ganin wanda za a buge da yake suna buga turmi biyu magariba ta yi, haka aka raba wasa, watakila a kara yin shi ranar Juma’a.

Watakila a ci gaba da wasannin gasar gwamnan jihar Kano a damben Kano da ya ƙunshi manyan ƴan wasa da ke fatan lashe ƙyautuga da yawa.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top