Da kyar idan Rashford zai koma Manchester United

An kusan kare wasannin bana a fannin tamaula, abin tambaya ko Marcus Rashford zai koma Manchester United?

Ɗan wasan tawagar Ingila ya koma buga wasannin aro zuwa karshen kakar bana, bayan da suka kasa cimma yarjejeniya da Aston Villa kan watan Janairu.

To sai dai Rashford na taka rawar gani a Barcelona ya kuma nuna karara cewar karsashi da farincikinsa sun dawo masa tun bayan da ya koma Barcelona da taka leda.

Tun lokacin da United ta ɗauki Ruben Amorim sabon kociyanta, dangan taka ta yi tsami tsakaninsu, inda mai horarwar ya sanar ba zai yi amfani da ɗan ƙwallon tawagar Ingila ba.

To sai dai kuma ƙungiyar Old Trafford ta kori Amorim daga baya ta maye gurbinsa da Micheal Carrick zuwa karshen kakar nan a matakin riƙon kwarya.

Carrick tsohon ɗan wasan United ya kai ƙungiyar mataki na uku a teburin Premier League, bayan cin wasa bakwai da canjaras ɗaya da rashin nasara ɗaya daga karawa tara da ya ja ragama.

Tuni Barcelona ke jin daɗin yadda Rashford ke saka ƙwazo a ƙungiyar, ana sa ran za ta sayi ɗan wasan, musamman da Joan Laporta ya kara cin zaɓen shugabancin ƙungiyar.

Kawo yanzu Rashford ya ci ƙwallo 10 da bayar da 13 aka zura a raga a dukkan karawa 38 tun bayan da ya koma Sifaniya da taka leda.

To sai dai kuma ɗan wasan na fama da ƙamfar cin ƙwallo, wanda rabon da ya ɗaga gidan kifi tun ranar 31 ga watan Janairu a wasan Elche a La Liga.

Tun daga lokacin bai kara cin ƙwallo a wasan da ya fuskanci Mallorca da Villareal da Atletic Bilbao a La Liga da karawa da Newcastle a Champions League.

Haka kuma bai ci ƙwallo ba a Copa del Rey da Barcelona ta buga da Albacete da Atletico Madrid.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top