Da kyar idan Palmer zai yi wa Chelsea karawa da Arsenal

Dan wasan Chelsea Cole Palmer bai yi atisaye ba ranar Litinin, sakamakon rashin lafiya da ya yi fama, kenan da kyar idan zai fuskaci Arsenal ranar Talata.

Arsenal za ta karbi bakuncin Chelsea a kwantan wasan Premier League a Emirates, wadanda suka tashi 2-2 a wasan farko a Stamford Bridge ranar 21 ga watan Oktoban 2023.

Palmer mai shekara 21 ya buga wa Chelsea FA Cup da Manchester City ta kai wasan karshe ranar Asabar da cin 1-0 a Wembley.

Rashin nasarar da Chelsea ta yi ya sa ba wani kofin da yake gabanta, illa tana fatan kammala kakar bana koda cikin ‘yan bakwai din din farko a Premier League, watakila ta samu gurbin shiga gasar zakarun Turai ta badi.

Palmer dan wasan tawagar Ingila, ya ci kwallo bakwai a wasa biyu baya a Stamford Bridge mai 20 a raga a Premier League, irin yawan wadanda Erling Haaland ya ci a kakar nan.

Liverpool ce ta doke Chelsea a wasan karshe a Carabao Cup, sannan Manchester City ta yi waje da ita a daf da karshe a FA Cup, wadda ba ta fafata a gasar zakarun Turai a kakar nan.

Idan Chelsea ta yi nasara a kan Arsenal, za ta hada maki iri daya da na Newcastle United ta shida, idan ta kara kwazo kafin kammala wasannin bana, watakila ta samu gurbin Europa League.

Arsenal ce ta daya a kan teburi da maki 74, iri da ya da na Liverpool da tazarar rarar kwallaye a tsakaninsu, Gunners na fatan lashe Premier League a bana, bayan kaka 20 rabonta da ta dauka.

Tuni dai Bayern Munich ta fitar da Arsenal daga Champions League na kakar nan a zagayen quarter finals.

Leave a comment