Da kyar idan Man United za ta je gasar zakarun Turai ta badi

Crystal Palace ta doke Manchester United 4-0 a wasan mako na 36 a Premier League da suka kara a Selhurst Park ranar Litinin.

Wannan shi ne karo na uku da suka fafata a bana, bayan da United ta ci 3-0 cikin Satumba, kwana hudu tsakani Palace ta ci 1-0 a Old Trafford.

Wadanda suka ci wa Palace kwallayen sun hada da Michael Olise da Jean-Philippe Mateta da Tyrick Mitchell da kuma Michael Olise.

Da wannan sakamakon United ta ci gaba da zama a mataki na takwas a teburin Premier League da maki 54 iri daya da na Chelsea ta bakwai, sai Newcastle United ta shida.

Ranar Lahadi Chelsea ta koma ta bakwai din teburi, bayan da ta caskara West Ham United 5-0 a wasan mako na 36 a Premier League.

Ita kuwa Palace ta hada maki 43 tana nan a matakinta na 14 a kasan teburi da tazarar maki daya tsakani da Fulham ta 13.

Kenan Manchester United na fatan kammala kakar bana a mataki na bakwai, domin ta samu shiga Europa Conference League a badi ko kuma ta doke Manchester City a FA Cup ta samu damar shiga Europa League a badi.

Wasa daya United ta yi nasara daga bakwai baya, hakan ne ya sa ta yi kasa zuwa ta takwas din teburi, wadda za ta karbi bakuncin Arsenal ranar Lahadi, sannan ta kara da Newcastle United ta rufe da zuwa gidan Brighton.

Leave a comment