Da kyar idan Haaland zai buga Fifa Club World Cup

Pep Gurdiola baya jin Erling Haaland zai murmure ya buga wa Manchester City gasar Premier League ranar Asabar.

Kociyan ya kara da cewar zai yi wuya Haaland ya yiwa kungiyar karawar da za ta yi a Fifa Club World Cup a mako mai zuwa a Saudi Arabia.

Sai a ranar 19 ga watan Disamba Manchester City mai rike da kofin zakarun Turai za ta buga daf da karshe a Fifa Club World Cup

Ranar Asabar Manchester City za ta karbi bakuncin Crysal Palace a wasan mako na 17 a Premier League.

Haaland wanda ya ci kwallo 19 kawo yanzu a bana, bai buga wa City wasan da ta doke Luton Town a Premier League da na Champions League da Red Star Belgrade ba.

Ranar Juma’a Haaland ya koma Manchester City, yayin da Guardiola ya ce likitoci za su auna koshin lafiyarsa, kafin ya yanke hukunci.

Ana sa ran Man City za ta ziyarci Saudi Arabia da zarar ta kammala wasan Premier da Palace ranar Asabar.

Leave a comment