Coventry City da Manchester United a FA Cup

Kociyan Coventry City, Mark Robins ya ce Manchester United ce take da damar kai wa zagayen karshe a FA Cup da za su kara ranar Lahadi zagayen daf da karshe a Wembley.

Kungiyar da ake kira Sky Blues na fatan samun shiga matakin cike gurbi a Championship, bayan da ta rasa maki uku daga wasa 12 baya.

A shekarar 1987 Coventry ta lashe FA Cup a karon farko, lokacin da ta doke Tottenham a karawar karshe, yayin da Manchester United ta dauki kofin karo 12 jimilla.

Manchester United aka doke a wasan karshe a bara a FA Cup, bayan da Manchester City ta dauki kofin, wadda ta kai zagayen karshe ranar Asabar, bayan cin Chelsea 1-0 a Wembley.

Kociya Erik ten Hag, wanda ya ja ragamar United ta doke Liverpool 4-3 a FA Cup a zagayen quarter final ta kai daf da karshe, bayan canjaras uku da rashin nasara daga wasa hudu da hakan ya sa ta koma ta bakwai a Premier League.

Ana sa ran Anthony da Scott McTominay za su koma taka leda daga jinyar da suka yi, haka shima Harry Maguire na daf da komawa buga wa Manchester United tamaula.

Leave a comment