Courtois ba zai buga wa Belgium Euro 2024 ba

Thibaut Courtois ba zai buga wa tawagar Belgium gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024 ba, sakamakon da bai koma kan ganiya ba.

Kociyan tawagar Belgium, Domenico Tedesco ne ya sanar da hakan da cewar golan baya kan ganiya da ya kamata ya tsare raga.

Courtois mai taka leda a Real Madrid bai yi wasa ko daya a kakar nan ba, ya koma atisaye amma ya fama raunin da ta kai an sake yi masa aiki a cikin watan Maris.

Courtois ya buga wa Jamus wasa 102, wadda ya fara tsarewa raga tun daga shekarar 2011, wanda tun cikin Disamba ya sanar cewar ba zai je gasar da Germany za ta karbi bakunci ba.

Tedesco ya sanar cewar aiki ya zo masa da sauki, bayan da Courtois ya sanar ba zai yi wa Jamus wasa ba, hakan ya sa tuni sun dauki madadinsa.

Ranar Litinin Courtois ya fara atisaye a Real Madrid, inda Carlo Ancelotti ya ce yana fatan golan zai buga musu La Liga a fafatawa da Cadiz.

Jamus za ta fara gudanar da gasar cin kofin nahiyar Turai daga 14 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yuli.

Leave a comment