Copa del Rey: Wasan karshe tsakanin Bilbao da Mallorca

Za a buga wasan karshe a Copa del Rey na bana tsakanin Athletic Bilbao da Real Mallorca ranar Asabar a filin wasa Estadio La Cartuja.

Athletic Bilbao ta kawo wannanzagayen bayan da ta doke Atletico Madrid 3-0 ranar 29 ga watan Fabrairu, ita kuwa Mallorca doke Real Sociedad ta yi 5-4 a bugun fenariri, bayan tashi 1-1 ranar 27 ga watan Fabrairu.

Sakamakon wasan La Liga da suka kara a bana tsakaninsu

Spanish La Liga Juma’a 2 ga watan Fabrairun 2024  

  • Ath Bilbao          4 – 0       Mallorca            

Spanish La Liga Lahadi 3 ga watan Satumbar 2023.  

  • Mallorca             0 – 0       Ath Bilbao

Bilbao ita ce ta biyu a yawan lashe Copa del Rey mai 23, Barcelona ce kan gaba mai 31, Real Madrid 20 ne da ita da Mallorca mai daya, wanda ta dauka a 2002/03.

Real Madrid ce mai rike da Copa del Rey na bara, bayan da ta ci Osasuna 2-1 ranar 6 ga watan Mayun 2023.

Leave a comment