China da Miami za su gudanar da Formula 1 a 2024

An sanar da cewar China da Miami za su dauki bakuncin tseren motocin Formula 1 a kakar 2024.

Karon farko da za su gudanar da tseren, yayin da Austria da Brazil za su yi karo na uku.

Filin wasa na Austin da na Qatar zai gabatar da tsere karo na biyu a badi, wato 2024.

A sabon tsarin za a yi atisaye rana daya wato Juma’a, sannan a gabatar da tseren Grand Fri ranar Lahadi.

Karon farko da China za ta gabatar da Formula 1 tun bayan 2019, daga nan aka soke wasannin sakamakon bullar cutar korona.

Leave a comment