Chelsea ta tuntubi RB Leipzig kan Lukeba

Wasu rahotanni na cewar Chelsea ta tuntubi RB Leipzig kan ko za a sayar mata da Castello Lukeba.

Dan wasan ya fara daga matasan Lyon daga baya ya yi mata wasa 68 tare da manyan ‘yan wasanta a Ligue 1.

Kwazon da dan wasan ya saka ne ya sa Leipzig ta dauki shi kan £30m, wanda ya koma Germany kan yarjejeniyar kaka biyar.

Mai shekara 21 yana cikin ‘yan wasan da Marco Rose ke fara karawa da su a Leipzig, wanda ya buga wasa 37 a dukkan karawa.

Haka kuma Lukeba ya yi wa Leipzig wasa bakwai baya, wadda ta hada maki 19 daga 21 dake kasa, wadda aka ci kwallo hudu a cikin karawar.

Koda yake kasa da kaka daya Lukeba ya yi a Leipzig, yanzu manyan kungiyoyi na son daukar dan kwallon har da na Premier League.

To sai dai Leipzig, tana ganin Lukeba a matakin daya daga fitattun ‘yan kwallonta, kenan zai yi wahala ta bari ya bar kungiyar cikin sauri.

Dan wasan mai tsaron baya yana da kunshin kwantiragin £60m da Leipzig ga duk kungiyar da take son sayen dan wasan idan yarjejeniyarsa bai kare ba.

Sai dai Chelsea za ta fuskanci kalubale daga Manchester United, wadda itama tana son tuntubar RB Leipzig ko za a sayar mata da dan kwallon.

© Reuters

Leave a comment