Champions League: Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye

Ranar Laraba aka kammala wasannin cikin rukuni a Champions League ta bana, an kuma samu 16 da za su buga zagaye na biyu.

Kungiyoyin da za su buga wasannin zagaye na biyu sun hada da Arsenal, Atlético Madrid, Barcelona, Bayern Munich, Copenhagen, Borussia Dortmund, Inter Milan, Lazio da kuma Leipzig.

Sauran sun hada da Napoli, Paris St Germain, Porto, PSV Eindhoven, Real Madrid, Real Sociedad da Manchester City mai rike da kofin bara.

Ranar Litinin 18 ga watan Disamba, hukumar kwallon kafar Turai, Uefa za ta gudanar da jadawalin zagaye na biyu.

Za a fara wasannin zagaye na biyu a Champions League daga 13 ko 14 ko 20 ko kuma 21 ga watan Fabrairu.

Wasa na biyu kuwa za a fafata ne tsakanin 5 ko 6 ko 12 ko kuma 13 ga watan Maris.

Jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Champions League a bana:

Masu kwallo biyar a raga:

  • Antoine Griezmann (Atlético Madrid)
  • Erling Haaland (Man City)
  • Rasmus Højlund (Man United)
  • Álvaro Morata (Atlético Madrid)

Masu kwallo hudu a raga:

  • Julián Álvarez (Man City)
  • Jude Bellingham (Real Madrid)
  • Evanilson (Porto)
  • Galeno (Porto)
  • Gabriel Jesus (Arsenal)
  • Harry Kane (Bayern)
  • Loïs Openda (Leipzig)
  • Danylo Sikan (Shakhtar)

Masu kwallo uku a raga:

  • João Félix (Barcelona)
  • Phil Foden (Man City)
  • Ciro Immobile (Lazio)
  • Joselu (Real Madrid)
  • Lukas Lerager (Copenhagen)
  • João Mário (Benfica)
  • Kylian Mbappé (Paris)
  • Brais Méndez (Real Sociedad)
  • Rodrygo (Real Madrid)
  • Bukayo Saka (Arsenal)
  • Ferran Torres (Barcelona)

Leave a comment