Champions League: Real Madrid da Bayern Munich

Bayern Munich za ta fuskanci Real Madrid a wasan daf da karshe a Champions Leageu ranar Talata a Allianz Arena.

Wasa na 27 da za su kara a tsakaninsu a gasar zakarun Turai karo na farko tun bayan 2018, inda Real ta ci 2-1 a Jamus a wasa na biyu suka tashi 2-2 a Spain.

Real Madrid ta doke Bayern Munich sau 12 da canjaras uku, ita kuwa kungiyar Germany ta ci karawa 11 a wasannin da suka fuskanci juna a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai.

Haka kuma wasa ne da fitattun ‘yan kwallon tawagar England za su fuskanci juna a tsakaninsu, wato Kyaftin Harry Kane da kuma Jude Bellingham.

Shi dai Kane ya ci kwallo 35 a Bundesliga a kakarsa ta farko daga Tottenham, shima Bellingham a wannan kakar ya fara yi wa Real wasa daga Borrussia Dortmund, mai kwallo 17 a raga a La Liga kawo yanzu.

Real Madrid mai Champions League 14 tana daf da daikar La Liga na bana na 36 jimilla, ita kuwa Bayern Munich mai kofin zakarun Turai shida ta rasa Bundesliga, bayan da Bayern Leverkusen ta lashe na farko a tarihin kungiyar, ta yi wa kungiyar da Thomas Tuchel ke jan ragama, bayan daukar 11 a jere.

‘Yan wasan Real Madrid da za suka je Germany:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Kepa.

Masu tsare baya: Carvajal, Militão, Alaba, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger, Mendy.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Ceballos, Arda Güler.

Masu cin kwallaye: Vini Jr., Rodrygo, Joselu, Brahim.

Leave a comment