Champions League: Ko Atletico za ta doke Dortmund?

Za a buga wasan zagayen farko a Champions League karawar quarter finals tsakanin Athletico Madrid da Borussia Dortmund ranar Laraba.

Wannan shi ne karo na bakawi da za su kara a tsakaninsu, inda kungiyar Germany ta yi nasara uku ta Spain ta ci biyu da canjaras daya a tsakaninsu.

Wasan karshe da suka fuskanci juna a Champions League shi ne a kakar 2018/19, inda Dortmund ta ci 4-0 ranar Laraba 24 ga watan Oktoba, Atletico ta yi nasarar cin 2-0 a wasa na biyu ranar Talata 6 ga watan Nuwamba.

Dortmund tana ta biyar a kan teburin Bundesliga, wadda ta kai quarter finals a Champions League karon farko bayan 2021.

Aatletico wadda ke karbar bakuncin Dortmund na fatan kai wa daf da karshe a karon farko tun bayan 2017.

Leave a comment