Champions League: Ancelotti ne na biyu a wasanni a Real Madrid

Carlo Ancelotti ya zama na biyu a matakin kociyan da ya fi yawan jan ragama a wasannin Champions League a Real Madrid.

Dan kasar Italy ya ja ragamar Real Madrid a wasan daf da karshe da Bayern Munich ranar Talata, fafatawa ta 61 kenan.

Vicente Del Bosque ne na uku mai wasa 60 da Miguel Muñoz na farko mai jan ragama karawa 71 a kungiyar Santiago Bernabeu.

Cikin wasa 61 da ya horar ya yi nasara 43 da canjaras 9 aka doke shi wasa 9, wanda ya lashe Champions League biyu a matakin kociyan Real Madrid a 2014 da kuma 2022.

Ancelotti ya kai daf da karshe karo biyar a Champions League a Real Madrid, kociyan dan kasar Italy ya ja ragamar wasa 200 a Champions League.

Kuma shi ne kadai ya lashe Champions League hudu jimilla a tarihi.

Haka kuma Ancelotti ya ja ragama wasa na 208 a Munich a gasar zakarun Turai, iri daya da yawan na Arsene Wenger, wanda ke kan gaba shi ne Sir Alex Ferguson mai 214 jimilla.

Bayern Munich da Real Madrid sun tashi 2-2 a wasan farko a daf da karshe a Champions League.

Real Madrid mai Champions League 14 za ta karbi baukun Bayern Munich mai shida jimilla ranar Laraba 8 ga watan Mayu.

Leave a comment