Cesena ta naɗa Ashley Cole sabon kociyanta

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Cesena mai buga gasar Italiya mai daraja ta biyu ta naɗa Ashley Cole a matakin sabon wanda zai horar da ita.

Tuni kuma tsohon ɗan wasan tawagar Ingila ya amince da yarjejeniyar zuwa karshen kakar nan, daga nan za a tantance ko za a bashi ƙungiyar ko kuma zai kara gaba.

Wannan shi ne karon farko da Cole tsohon ɗan wasan Chelsea zai fara aiki a matakin koci, bayan da ya yi mataimaki a Derby Conte da Everton da Birmingham da kuma tawagar Ingila.

Kawo yanzu Cesena tana mataki na takwas a kan teburin Serie B, wadda ta ci karo da koma baya da kasa cin wasa daga bakwai baya, wadda ta yi rashin nasara huɗu da canjaras uku.

Cole ya buga wa Ingila wasa 107 ya kuma yi ritaya a 2019 a Derby County daga nan ya shiga sabbar horar da tamaula.

Tsohon ɗan wasan ya lashe kofi 13 daga ciki har da Premier League uku da FA Cup bakwai da League Cup da Champions League da Europa League a Chelsea.

Cole ya bar ƙungiyar Stamford Bridge ya koma Roma ta Italiya a 2014 da yi mata wasa 16 a babbar gasar tamaula ta Italiya.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top