Carvalho ya koma Liverpool tun kan ya kare wasannin aro a Leipzig

Fabio Carvalho ya bar RB Leipzig ya koma Liverpool tun kan yarjejeniyar buga wasannin aro a Jamus ya kare, kamar yadda kungiyoyin biyu suka sanar.

Carvalho ya koma Leipzig domin buga wasannin aro kan fara kakar bana, ya yi mata karawa 15 daga ciki aka fara wasa uku da shi a cikin fili.

Liverpool, wadda take matakin farko a teburin Premier League za ta karbi bakuncin Newcastle United a Anfield ranar Litinin.

Ranar 27 ga watan Agusta Liverpool ta yi nasara a kan Newcastle da cin 2-1 a St James Park.

Newcastle mai mai maki 29 tana ta tara a teburin Premier League.

Leave a comment