Carvajal zai yi jinya zuwa karshen shekara

Dan wasan Real Madrid, Dani Carvajal zai yi jinya zuwa karshen shekaran nan, kamar yadda kungiyar ta sanar ranar Litinin.

Mai tsaron bayan ya ji rauni a wasan da Real Madrid ta doke Granada a gasar La Liga ranar Asabar.

An sauya dan kwallon tawagar Spain a karawar da Real Madrid ta ci 2-0.

Da wannan sakamakon Real ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga da maki 38, iri daya da na Girona ta biyu.

Bayan da likitoci suka auna girman raunin da dan kwallon ya ji, bas u fayyace ranar da zai koma taka led aba.

Sai dai wasu jaridun Spain na cewar Carvajal zai yi jinyar wata daya.

Mai shekara 31 ya buga wa Real Madrid wasanni da yawa a bana, wanda ya yi mata kaftin karo da yawa.

Leave a comment