Alcaraz ya rasa kocinsa Ferrero kafin Australian Open.

Carlos Alcaraz zai yi babban rashi a gasar Grand Slam ta farko a shekarar 2024 bayan ya rasa kocinsa Juan Carlos Ferrero kafin gasar Australian Open.

Alcaraz yana cikin shirin share fage na makonni biyar – wanda ya fara a ranar 8 ga Disamba – don tabbatar da cewa yana cikin yanayi mai kyau a gasar Melbourne a watan Janairu.

Amma zai kammala shirye-shiryensa ba tare da Ferrero ba, wanda ba zai iya tafiya ba bayan an tabbatar da cewa yana bukatar tiyatar arthroscopic a gwiwarsa ta hagu.

Samuel Lopez ne zai maye gurbin tsohon dan wasan kwallon Tennis na tsawon makonni biyu, saboda Ferrero zai bukaci yin tafiya da sanda bayan tiyatar.

Amma Alcaraz yana hannun Lopez, wanda shine kocin dan wasan Spain Pablo Carreno Busta kuma gogaggen mai horarwa.

Leave a comment