Caf ta bai wa Morocco kofin da Senegal ta lashe na Afcon 2026

Hukumar ƙwallon kafa ta Afirka Caf, ta bai wa Morocco kofin Afcon, wanda Senegal ta lashe a 2026.

Hakan ya biyo bayan shigar da kara da hukumar ƙwallon kafar Morocco ta yi, bisa fita daga fili da Senegal ta yi, saboda an bai wa mai masukin baƙi bugun fenariti.

Koda yake Senegal ta koma an ci gaba da fafatawar da aka yi ranar 18 ga watan Janairun 2026 daga baya ta ci ƙwallo aka tashi tana da 1-0.

Minti 17 aka ɓata kafin a ci gaba da karawar, inda Brahim Diaz na Morocco ya ɓarar da fenaritin kafin daga baya Senegal ta ci ƙwallo ta hannun Pape Gueye.

Sai dai kawo yanzu wannan sakamakon ya sauya, bayan da Caf ta ce Morocco ce ta zama zakara da cin 3-0 a hukuncin da ta yanke, sakamakon shigar da kara da wadda ta shirya Afcon ta yi.

Caf ta sanar cewar tawagar Senegal ta karya dokarta ta sashi na 82 na gasar cin kofin nahiyar Afirka, saboda haka an yanke mata hukunci kan doka ta sashi na 84.

Dota ta sashi na 82 ta Caf ta ce duk tawagar da ta fita daga fili kafin lokacin tashi ya cika ba tare da amincewar rafli ba, za a dauka ta rasa wasan, kuma za a koreta daga gasar.

Saboda haka hukuncin sashe na 84 ya ce duk tawagar da ta karya dokar sashe na 82, za a kore ta daga gasar, sannan an doke ta 3-0 a sakamakon karawar.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top