Brighton ta yi kokarin sayen Palmer daga Man City a bara

Kociyan Brighton, Roberto de Zerbi ya ce ya yi korarin daukar Cole Palmer daga Manchester City a bara.

Palmer ya zama kashin bayan Chelsea a kakar bana, bayan da kungiyar Stamford Bridge ta saye shi kan £42.5m daga City a Satumbar 2023.

Mai shekara 22 ya ci kwallo 21 ya bayar da 10 aka zura a raga a wasa 31 a Premier League, yayin da Chelsea za ta fuskanci Brighton a kwantan wasan mako na 34 ranar Laraba.

De Zerbi ya sanar cewar Chelsea ta yi dace da ta samu matashin dan wasan, domin yana sa kaimi a dukkan wasannin da yake bugawa.

De Zerbi ya ja kunnen ‘yan wasan Brighton su kulla da Palmer duk motisin da zai yi, domin zai yi kokarin cin kwallo, zai kuma iya yi musu sakiyar da ba ruwa.

Leave a comment