Brazil tana zaman makokin mutuwar Mario Zagallo

Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva ya jagorancin zaman makokin mutuwar Mario Zagallo, mai shekara 92.

Zagallo, wanda ya taka leda tare da Pele a tawagar Brazil da ta lashe kofin duniya a 1958 da kuma 1962 ya mutu ranar Juma’a.

Ya horar da Brazil a 1970 ya kuma lashe kofin duniya a lokacin, sannan ya yi mataimakin koci a 1994 da tawagar ta kara daukar kofin.

Kenan Zagallo yana da hannu a daukar kofi hudu daga biyar da Brazil ta lashe a gasar cin kofin duniya.

Wasu da suka lashe kofin duniya a matakin dan wasa da koci sun hada da dan kasar Jamus, Franz Beckenbauer a 1974 da 1990 da kuma dan kasar Faransa, Didier Deschamps a 1998 da kuma 2018.

Hukumar kwallon kafar Brazil ta bayar da hutun mako daya da yin shiru na minti daya a lokacin wasannin gasar kasar na gaba.

Suma kungiyoyin da Zagallo ya taka leda sun yi zaman makoki da suka hada da Botafogo da Fluminense da kuma Vasco.

Har da kungiyar da Zagallo bai taka leda ba da suka hada da Santos, kungiyar da Pele ya taka leda, wanda ya mutu a Disambar 2022 yana da shekara 82.

Ranar Juma’a Brazil ta kori, Fernando Diniz, bayan da tawagar take ta shidan teburi a wasannin neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026.

Tun farko Brazil ta sa ran daukar Carlo Ancelotti, sai dai a watan jiya kociyan ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da horar da Real Madrid.

Leave a comment