Bologna na daf da samun gurbin Champions League

Kungiyar Bologna na daf da samun gurbin shiga Champions League a badi, bayan da ta yi nasara a kan Napoli a gasar Serie A.

Wadanda suka ci mata kwallayen sun hada da Dan Ndoye da Stefan Posch da kungiyar da Thiago Motta ke jan ragama ta koma ta uku a saman Juventus da tazarar maki bakwai tsakani da Roma.

Kungiyoyi biyar din farko a kakar bana a Serie A ne za su wakilci Italya a gasar badi.

Atalanta ce ta biyar a teburi da kuma Roma ta shida, kenan Bologna na bukatar cin wasa daya ta samu gurbi Champions League kai tsaye.

Bologna ta buga wasa daya a tsohuwar gasar zakarun Turai a 1964 a kakar ta lashe kofin lik na bakwai, amma ba ta taba samun zuwa buga Champions League ba.

To sai dai dan wasan Bologna, Joshua Zirkzee ya ji ciwo a karawar, hakan zai zama koma baya a kungiyar.

Leave a comment