Bilbao ta lashe Copa del Rey babban kofi bayan shekara 40

Athletic Bilbao ta lashe Copa del Rey na bana bayan nasara a kan Real Mallorca a bugun fenariti, babban kofi da ta dauka bayan shekara 40.

Ta dauki Copa del Rey na 24 jimilla, kuma na farko tun bayan 1984, bayan da ta yi nasara a kan Sevilla a karawar karshe a gasar.

Tun farko sun tashi 1-1 a karawar da suka yi a La Cartuja ranar Asabar, inda Dani Rodriguez ya fara ci wa Mallorca kwallo daga baya Athletic Club ta farke ta hannun Oihan Sancet.

Mallorca mai buga gasar Spain mai daraja ta uku tun daga 2018 ta yi fatan daukar Copa del Rey karo na biyu a tarihin, bayan lashe na shekarar 2003.

Athletic Club ta yi nasarar lashe kofin a bugun daga kai sai mai tsaron raga, inda ta ci kwallo 4-2.

Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Copa del Rey mai 31 jimilla, sai Athletic Club mai 24, yayin da Real Madrid take da 20 jimilla.

Leave a comment